13 Faburairu 2022 - 13:41
EU Da Iran Na Ci Gaba Da Tattaunawa A Vienna

Tawagogin Iran da Tarayyar Turai sun gana a Vienna, inda suka ci gaba da tattaunawa mai zurfi a zagaye na takwas na tattaunawa tsakanin Iran da kasashen da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shafa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kuma babban mai shiga tsakani a tattaunawar, Ali Bagheri Kani, da Enrique Mora, mukadashin shugaban kula da manufofin kungiyar Tarayyar Turai sun gana a ranar Asabar.

Har ila yau, an gudanar da taron tattaunawa tsakanin kasashen Iran da Rasha a karkashin jagorancin Bagheri Kani da Mikhail Ulyanov, a babban birnin kasar Ostiriya.

Bangarorin dai sun dukufa wajen rubuta yarjejeniyar da kuma yanke shawara kan wasu batutuwan da suka rage.

Kafin hakan, masana daga Iran da kasashen gungun na P4+1 sun gana a ranar Juma'a a kwamitin aiki guda uku na tattauna batutuwan da suka shafi nukiliya, dage takunkumi da kuma shirye-shiryen zartarwa don tinkarar sauran batutuwan da suka rage a tattaunawar ta Vienna.

342/